<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>John Newton</author>
<lyrics>[V1]
 1) Alherin Ubangijina abin mamaki ne.
 Yesu ya ba da jininsa pansar mai zunubi,
 Pansar mai zunubi.

[V2]
 2) Tun ranar da na tuba fa, alherinsa 'na nan.
 Alheri kuwa zai kai ni can wurin Ubangiji,
 Wurin Ubangiji.

[V3]
 3) Ya raina, kar ka manta dai da duk alherinsa.
 Abu duk da ke cikina ya yabi sunansa, Ya yabi sunansa.

[V4]
 4) Ubangiji da tausayi da jinkirin fushi ne.
 Alherinsa tun farko ne a kan mai tsoronsa,
 A kan mai tsoronsa.

[V5]
 5) Me zan bayar, Ubangiji, domin alherinka?
 Zan miƙa jiki hadaya tare da zuciyata,
 Tare da zuciyata.

[V6]
 6) Ruhun Alheri, zuga ni, tsabtad da gurina.
 Iyad da ni don aiki na shelar bishararka,
 Shelar bishararka.</lyrics>
<title>Alherin Ubangijina Abin Mamaki Ne LW301</title>
<hymn_number>301</hymn_number>
</song>